ZAB 143

Addu’ar Neman Ceto da Kiyayewa

1 Ya Ubangiji ka ji addu’ata,

Ka kasa kunne ga roƙona!

Kai adali ne mai aminci,

Don haka ka amsa mini!

2 Ni bawanka, kada ka gabatar da ni a gaban shari’a,

Gama ba wanda ba shi da laifi a gare ka.

3 Maƙiyina ya tsananta mini,

Ya kore ni fata-fata.

Ya sa ni a kurkuku mai duhu,

Ina kama da waɗanda suka daɗe da mutuwa,

4 Don haka ina niyya in fid da zuciya,

Ina cikin damuwa mai zurfi.

5 Na tuna kwanakin baya,

Na tuna da dukan abin da ka yi,

Na tuna da dukan ayyukanka.

6 Na ɗaga hannuwana sama, ina addu’a gare ka,

Kamar busasshiyar ƙasa, raina yana jin ƙishinka.

7 Yanzu ka amsa mini, ya Ubangiji!

Na fid da zuciya duka!

Kada ka ɓuya mini,

Don kada in zama cikin waɗanda suke gangarawa zuwa lahira.

8 A gare ka nake dogara,

Da safe ka tuna mini da madawwamiyar ƙaunarka.

Addu’ata ta hau zuwa gare ka,

Ka nuna mini hanyar da zan bi.

9 Na tafi wurinka don ka kiyaye ni, ya Ubangiji,

Ka cece ni daga maƙiyana.

10 Kai ne Allahna,

Ka koya mini in aikata nufinka.

Ka sa in sami alherin Ruhunka.

Ka bi da ni a hanyar lafiya.

11 Ka cece ni, ya Ubangiji, kamar yadda ka alkawarta.

Saboda alherinka ka tsamo ni daga wahalaina!

12 Saboda ƙaunar da kake yi mini,

Ka kashe maƙiyana.

Ka hallakar da dukan waɗanda suke zaluntata.

Gama ni bawanka ne.