ZAB 142

Addu’ar Neman Taimako

1 Ina kira ga Ubangiji don neman taimako,

Ina roƙonsa.

2 Na kawo masa dukan koke-kokena,

Na faɗa masa dukan wahalaina.

3 Sa’ad da na yi niyyar fid da zuciya,

Ya san abin da zan yi.

A kan hanyar da zan bi

Maƙiyana sun kafa mini tarko a ɓoye.

4 Na duba kewaye da ni, sai na ga ba ni da wanda zai taimake ni,

Ba wanda zai kiyaye ni,

Ba kuwa wanda ya kula da ni.

5 Ya Ubangiji, na kawo kuka gare ka na neman taimako,

Ya Ubangiji, kai ne mai kiyaye ni,

Kai kaɗai nake so a rayuwata duka.

6 Ka kasa kunne ga kukana na neman taimako,

Gama na nutsa cikin fid da zuciya.

Ka cece ni daga maƙiyana

Waɗanda suka fi ƙarfina.

7 Ka cece ni daga cikin wahalata,

Sa’an nan zan yabe ka cikin taron jama’arka,

Domin ka yi mini alheri.