ZAB 149

Bari Isra’ilawa su Yabi Ubangiji

1 Yabo ya tabbata ga Ubangiji!

Ku raira sabuwar waƙa ga Ubangiji

Ku yabe shi cikin taron jama’arsa masu aminci!

2 Ki yi murna, ke Isra’ila, sabili da Mahaliccinki,

Ku yi farin ciki, ku jama’ar Sihiyona, sabili da Sarkinku!

3 Ku yabi sunansa, kuna taka rawa,

Ku kaɗa bandiri da garayu, kuna yabonsa.

4 Ubangiji yana jin daɗin jama’arsa,

Yakan girmama mai tawali’u ya sa ya ci nasara.

5 Bari jama’ar Allah su yi farin ciki saboda cin nasararsu,

Su raira waƙa don farin ciki.

6 Bari su yi sowa da ƙarfi

Sa’ad da suke yabon Allah, da takubansu masu kaifi.

7 Don su ci nasara bisa al’ummai,

Su kuma hukunta wa jama’a,

8 Su ɗaure sarakunansu da sarƙoƙi,

Su ɗaure shugabanninsu da sarƙoƙin baƙin ƙarfe,

9 Su hukunta wa al’ummai, kamar yadda Allah ya umarta.

Wannan shi ne cin nasarar jama’ar Allah!

Yabo ya tabbata ga Ubangiji!