ZAB 150

Ku Yabi Ubangiji

1 Yabo ya tabbata ga Ubangiji!

Ku yabi Allah a cikin Haikalinsa!

Ku yabi ƙarfinsa a sama!

2 Ku yabe shi saboda manyan abubuwa

Waɗanda ya aikata!

Ku yabi mafificin girmansa!

3 Ku yabe shi da kakaki!

Ku yabe shi da garayu da molaye!

4 Ku yabe shi da bandiri kuna taka rawa!

Ku yabe shi da garayu da sarewa!

5 Ku yabe shi da kuge!

Ku yabe shi da kuge masu amo!

6 Ku yabi Ubangiji dukanku rayayyun talikai.

Yabo ya tabbata ga Ubangiji!