ZAB 46

Allah ne Mafakarmu da Ƙarfinmu

1 Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu,

Kullum a shirye yake yă yi taimako a lokacin wahala.

2 Saboda haka ba za mu ji tsoro ba,

Ko da duniya za ta girgiza,

Duwatsu kuma su fāɗa cikin zurfafan teku,

3 Ko da a ce tekuna za su yi ruri su tumbatsa,

Tuddai kuma su girgiza saboda tangaɗin tekun.

4 Akwai kogin da yake kawo farin ciki a birnin Allah,

Da cikin tsattsarkan Haikali na Maɗaukaki.

5 Allah yana zaune cikin birnin,

Ba kuwa za a hallaka birnin ba, faufau.

Da asuba Allah zai kawo musu gudunmawa.

6 An kaɓantar da sauran al’umma, mulkoki suka girgiza,

Allah ya yi tsawa, duniya kuwa ta narke.

7 Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu,

Allah na Yakubu shi ne mafakarmu!

8 Zo ku ga abin da Ubangiji ya yi!

Dubi irin ayyukan al’ajabi da ya yi a duniya!

9 Ya hana yaƙoƙi ko’ina a duniya,

Yana karya bakkuna, yana lalatar da māsu,

Yana ƙone karusai da wuta.

10 Ya ce, “Ku yi shiru, ku sani ni ne Allah,

Maɗaukaki ne cikin sauran al’umma,

Maɗaukaki kuma a duniya!”

11 Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu,

Allah na Yakubu shi ne mafakarmu!