ZAB 47

Allah ne Mai Mulkin Duka

1 Ku yi tāfi saboda farin ciki,

Ya ku jama’a duka!

Ku raira waƙoƙi da karfi, ku yabi Allah!

2 A ji tsoron Ubangiji Mai Iko Dukka,

Shi babban Sarki ne, ya mallaki dukan duniya.

3 Ya ba mu nasara a bisa jama’o’i,

Ya sa muka yi mulkin al’ummai,

4 Ya zaɓar mana ƙasar da muke zaune,

Wadda take mallaka ce ta fāriya, ta jama’arsa

Wadda yake ƙauna.

5 Allah ya hau kan kursiyinsa!

Aka yi ta sowa ta murna, ana ta busa ƙahoni,

Lokacin da Ubangiji yake hawa!

6 Ku raira yabbai ga Allah,

Ku raira yabbai ga sarkinmu!

7 Allah sarki ne na duniya duka,

Ku yabe shi da waƙoƙi!

8 Allah yana zaune kan kursiyinsa mai tsarki,

Yana mulkin al’ummai,

9 Masu mulkin al’ummai suka tattaru

Tare da jama’ar Allah na Ibrahim.

Allah shi ne garkuwar jarumawa,

Yana mulkin duka!