ZAB 48

Sihiyona Mai Daraja, Birnin Allah

1 Ubangiji mai girma ne,

Dole kuwa a yabe shi da girmamawa a birnin Allahnmu,

A kan tsattsarkan dutsensa.

2 Dutsen Sihiyona, dutse mai tsawo,

Mai kyan gani ne na Allah,

Birnin babban Sarki.

Yakan kawo farin ciki ga dukan duniya!

3 Allah ya nuna akwai zaman lafiya a wurinsa,

A kagarar birnin.

4 Sarakuna suka tattaru,

Suka zo Dutsen Sihiyona,

5 Da suka gan shi sai suka yi mamaki,

Suka tsorata suka gudu.

6 Tsoro ya kama su suka razana,

Kamar mace wadda take gab da haihuwa.

7 Allah yakan hallaka manyan jiragen ruwa da iskar gabas.

8 Mun ji labarin waɗannan al’amura,

Yanzu kuwa mun gan su

A birnin Allahnmu, Mai Runduna,

Zai kiyaye birnin lafiya har abada.

9 A cikin Haikalinka, ya Allah,

Muna tunanin madawwamiyar ƙaunarka.

10 A ko’ina jama’a suna yabonka,

Sunanka ya game duniya duka.

Kana mulki da adalci.

11 Bari jama’ar Sihiyona su yi murna!

Gama kana shari’a ta gaskiya,

Bari biranen Yahuza su yi farin ciki.

12 Ku tafi ku kewaye Dutsen Sihiyona,

Ku ƙirga yawan hasumiyarsa.

13 Ku lura da garukanta, ku bincike kagaranta,

Saboda ku iya faɗa wa tsara mai zuwa,

14 Cewa wannan Allah shi ne Allahnmu har abada abadin,

Shi ne zai bishe mu a dukan zamanai masu zuwa.