ZAB 60

Addu’ar Neman Taimako

1 Ka rabu da mu, ya Allah, har aka ci nasara a kanmu,

Ka yi fushi da mu, amma yanzu sai ka juyo wurinmu!

2 Ka sa ƙasar ta girgiza, ka tsaga ta.

Yanzu sai ka warkar da tsaguwarta, gama tana gab da fāɗuwa!

3 Ka sa jama’arka su sha wahala ƙwarai,

Ka ba mu ruwan inabin da ya bugar da mu.

4 Ka ta da tuta ga masu tsoronka,

Domin su juya su gudu daga abokin gāba.

5 Ka cece mu da ƙarfinka, ka amsa addu’ata,

Domin jama’ar da kake ƙauna ta sami cetonka.

6 A tsattsarkan wurinsa, Allah ya faɗa ya ce,

“Da nasara zan raba Shekem,

Da nasara kuma zan rarraba Sukkot ga jama’ata.

7 Gileyad tawa ce, har da Manassa ma,

Ifraimu ne kwalkwalina,

Yahuza kuma sandana ne na sarauta.

8 Amma zan yi amfani da Mowab kamar kwanon wanki,

Edom kuwa kamar akwatin takalmina.

Zan yi sowar nasara a kan Filistiyawa.”

9 Ya Allah, wa zai kai ni birni mai kagara?

Wa zai kai ni Edom?

10 Da gaske ka yashe mu ke nan?

Ba za ka yi tafiya tare da sojojinmu ba?

11 Ka taimake mu, mu yaƙi abokan gāba,

Domin taimako irin na mutum banza ne!

12 Idan Allah yana wajenmu,

Za mu yi nasara,

Zai kori abokan gābanmu.