ZAB 61

Dogara ga Kiyayewar Allah

1 Ya Allah, ka ji kukana,

Ka ji addu’ata!

2 Sa’ad da nake nesa da gida, zuciyata ta karai,

Zan yi kira gare ka!

Ka kai ni lafiyayyiyar mafaka.

3 Kai ne kāriyata mai ƙarfi

Da take kiyaye ni daga maƙiyana.

4 Ka yarda in zauna a alfarwarka dukan kwanakin raina,

Ka yarda in sami zaman lafiya a ƙarƙashin fikafikanka.

5 Ya Allah, kā ji alkawaraina,

Kā kuwa ba ni abin da ya dace,

Tare da waɗanda suke ɗaukaka ka.

6 Ka ƙara wa sarki tsawon rai,

Ka sa ya rayu dukan lokaci!

7 Ka sa ya yi mulki har abada a gabanka, ya Allah,

Ka tsare shi da madawwamiyar ƙaunarka, da amincinka.

8 Don haka zan yi ta raira waƙar yabonka kullayaumin,

A sa’ad da nake miƙa maka abin da na alkawarta.