ZAB 66

Waƙar Yabo da Miƙa Hadaya ta Godiya

1 Ku yabi Allah da babbar murya ta farin ciki,

Ya jama’a duka!

2 Ku raira waƙar darajar sunansa,

Ku yabe shi da ɗaukaka!

3 Ku faɗa wa Allah cewa, “Al’amuran da kake aikatawa

Suna da banmamaki ƙwarai!

Ikonka yana da girma ƙwarai,

Har maƙiyanka sukan durƙusa a gabanka don tsoro.

4 Duk wanda yake a duniya, yana yi maka sujada,

Yana raira maka waƙar yabbai,

Yana raira yabbai ga sunanka.”

5 Zo, ka ga abin da Allah ya yi,

Ayyukansa masu ban al’ajabi

Waɗanda ya aikata ga mutane.

6 Ya sa teku ta zama busasshiyar ƙasa,

Kakanninmu suka haye kogi da ƙafa.

A can muka yi farin ciki saboda abin da ya yi.

7 Har abada yana mulki ta wurin ƙarfinsa,

Yana duban al’ummai,

Don kada ‘yan tawaye su tayar masa!

8 Ku yabi Allahnmu, ya ku dukan al’ummai,

Bari a ji yabon da kuke yi masa.

9 Shi ne yake rayar da mu,

Bai kuwa yarda mu fāɗi ba.

10 Ka jarraba mu, ya Allah,

Kamar yadda ake tace azurfa da wuta,

Haka nan ka jarraba mu.

11 Ka bar mu muka fāɗa a tarko,

Ka ɗora mana kaya masu nauyi.

12 Ka bar maƙiyanmu suka tattaka mu,

Mun ratsa ta cikin wuta da rigyawa,

Amma yanzu ka kawo mu a lafiyayyen wuri.

13 Zan kawo hadayun ƙonawa a ɗakinka,

Zan miƙa maka abin da na alkawarta.

14 Zan ba ka abin da na ce zan bayar,

A lokacin da nake shan wahala.

15 Zan miƙa tumaki don a ƙona a kan bagade,

Nan za a ji ƙanshi mai daɗi na ƙonannun awaki,

Zan miƙa hadayu na bijimai da na awaki.

16 Ku zo ku ji, dukanku, ku da kuke girmama Allah,

Ni kuwa zan faɗa muku abin da ya yi mini.

17 Na yi kira gare shi neman taimako,

A shirye nake in yabe shi da waƙoƙi.

18 Da ban watsar da zunubaina ba,

Da Ubangiji bai ji ni ba.

19 Amma hakika Allah ya ji ni,

Ya saurari addu’ata.

20 Ina yabon Allah,

Domin bai ƙi addu’ata ba,

Bai kuwa hana mini madawwamiyar ƙaunarsa ba.