ZAB 67

Waƙar Miƙa Hadaya ta Godiya

1 Ka yi mana jinƙai, ya Allah, ka sa mana albarka,

Ka dube mu da idon rahama,

2 Domin dukan duniya ta san nufinka,

Dukan sauran al’umma kuma su san cetonka.

3 Da ma dukan mutane su yabe ka, ya Allah,

Da ma dukan mutane su yabe ka!

4 Da ma sauran al’umma su yi murna, su raira waƙa ta farin ciki,

Domin kana yi wa jama’a shari’a ta adalci,

Kana kuma bi da dukan sauran al’umma.

5 Da ma dukan mutane su yabe ka, ya Allah,

Da ma dukan mutane su yabe ka!

6 Ƙasa ta ba da amfaninta,

Allah, wanda yake Allahnmu ne, ya sa mana albarka.

7 Allah ya sa mana albarka,

Da ma dukan jama’a ko’ina su girmama shi.