ZAB 74

Addu’ar Neman Ceton Al’ummar Allah

1 Don me ka yashe mu haka, ya Allah?

Za ka yi ta fushi da jama’arka har abada ne?

2 Ka tuna da jama’arka waɗanda ka zaɓa su zama naka tuntuni,

Ka tuna da jama’arka waɗanda ka fansa,

Don su zama kabilarka.

Ka tuna da Dutsen Sihiyona, inda zatinka yake!

3 Ka zo, ka yi yawo a wannan kufai,

Abokan gābanmu sun lalatar da kome na cikin Haikali!

4 Abokan gābanka suka yi sowa ta nasara

A inda akan sadu da kai,

Sun ƙwace Haikalin.

5 Suna kama da masu saran itace,

Suna saran itatuwa da gaturansu.

6 Da gaturansu da gudumarsu,

Sun ragargaje ƙyamaren da aka yi da katako.

7 Sun sa wa Haikalinka wuta,

Sun ƙazantar da wurin da akan yi maka sujada,

Sun farfashe shi duk.

8 Sun yi niyya su murƙushe mu sarai,

Sun ƙone kowane tsattsarkan wuri na ƙasar.

9 Ba sauran tsarkakan alamu,

Ba sauran annabawan da suka ragu,

Ba kuwa wanda ya san ƙarewar wannan.

10 Ya Allah, har yaushe abokan gābanmu za su yi ta yi mana ba’a?

Za su yi ta zargin sunanka har abada ne?

11 Me ya sa ka ƙi taimakonmu?

Ka tasar musu ka hallaka su!

12 Amma ya Allah, kai ne Sarkinmu tun daga farko,

Ka yi nasara da duniya.

13 Da ƙarfin ikonka ka raba teku,

Ka farfashe kawunan dodannin ruwa,

14 Ka ragargaje kawunan kadduna,

Ka kuwa ba mutanen hamada su ci.

15 Ka sa ruwan maɓuɓɓugai ya yi gudu,

Ka sa manyan koguna su ƙafe.

16 Ka halicci yini da dare,

Ka sa rana da wata a wurarensu.

17 Ka yi wa duniya kan iyaka,

Ka kuwa yi lokatan damuna da na rani.

18 Amma ka tuna fa, ya Ubangiji, abokan gābanka suna yi maka ba’a,

Su wawaye ne waɗanda suke raina ka.

19 Kada ka ba da jama’arka marasa taimako

A hannun mugayen maƙiyansu,

Kada ka manta da jama’arka waɗanda ake tsananta musu!

20 Ka tuna da alkawarin da ka yi mana,

Akwai tashin hankali a kowane lungu mai duhu na ƙasar!

21 Kada ka bari a kori waɗanda ake zalunta,

Amma bari matalauta da masu mayata su yabe ka.

22 Ka tashi, ya Allah, ka kāre kanka!

Ka tuna fa, marasa tsoronka suna ta yi maka ba’a dukan yini!

23 Kada ka manta da hargowar maƙiyanka,

Kada ka manta da hayaniyar da magabtanka suke ta yi.