ZAB 76

Allah Mai Nasara Mai Hukunci

1 Allah sananne ne a Yahuza,

Mashahuri ne kuma a Isra’ila.

2 Wurin zamansa yana Urushalima,

A dutsen Sihiyona zatinsa yake.

3 A can yake kakkarya kiban abokan gāba,

Da garkuwoyinsu, da takubansu, i, har da dukan makamansu.

4 Ina misalin darajarka, ya Allah!

Ina misalin ɗaukakarka a sa’ad da ka komo daga kan duwatsu,

Daga korar abokan gābanka!

5 An kwashe ganimar sojojinsu masu ƙarfin hali,

Yanzu suna barci, barcin matattu,

Ba waninsu da ya ragu,

Da zai yi amfani da makamansa.

6 Sa’ad da ka fafare su, ya Allah na Yakubu,

Dawakansu da mahayansu suka fāɗi matattu.

7 Amma mutane suna jin tsoronka!

Wa zai iya tsayawa a gabanka

Sa’ad da ka yi fushi?

8 Daga Sama ka sanar da shari’arka,

Duniya ta tsorata, ta yi tsit,

9 Sa’ad da ka tashi domin ka yanke hukunci,

Domin ka ceci waɗanda ake zalunta a duniya.

10 Hasalar mutane ba ta ƙara kome, sai dai ta ƙara maka yabo.

Waɗanda suka tsira daga yaƙe-yaƙe za su kiyaye idodinka.

11 Ku ba Ubangiji Allahnku abin da kuka alkawarta masa,

Dukanku sauran al’umma da kuke kusa, ku kawo masa kyautai.

Allah yakan sa mutane su ji tsoronsa,

12 Yakan ƙasƙantar da shugabanni masu girmankai,

Ya tsoratar da manyan sarakuna.