ZAB 80

Addu’ar Komo da Al’umma

1 Ka kasa kunne gare mu, ya Makiyayin Isra’ila,

Ka ji mu, kai da kake shugaban garkenka,

Da kake zaune a kan kursiyinka, a bisa kerubobi.

2 Ka bayyana ƙaunarka ga kabilar Ifraimu,

Da ta Biliyaminu, da ta Manassa!

Ka nuna mana ikonka,

Ka zo ka cece mu!

3 Ka komo da mu, ya Allah!

Ka nuna mana ƙaunarka, za mu kuwa cetu!

4 Har yaushe ke nan ya Ubangiji Allah Mai Runduna,

Za ka yi ta fushi da addu’o’in jama’arka?

5 Ka ciyar da mu da hawaye,

Ka shayar da mu da babban ƙoƙo na hawaye.

6 Ka bar al’umman da take makwabtaka da mu

Su yi ta faɗa a kan ƙasarmu,

Abokan gābanmu kuma suna yi mana ba’a.

7 Ka komo da mu, ya Allah Mai Runduna!

Ka nuna mana ƙaunarka, za mu kuwa cetu!

8 Ka fito da kurangar inabi daga cikin Masar,

Ka kori sauran al’umma,

Ka dasa kurangar a ƙasarsu.

9 Ka gyara mata wuri don ta yi girma,

Saiwoyinta suka shiga ƙasa sosai,

Ta yaɗu, ta rufe dukan ƙasar.

10 Ta rufe tuddai da inuwarta,

Ta rufe manya manyan itatuwan al’ul da rassanta.

11 Rassanta sun miƙe har Bahar Rum,

Har zuwa Kogin Yufiretis.

12 Me ya sa ka rushe shingen da yake kewaye da ita?

Ga shi yanzu, duk mai wucewa yana iya satar ‘ya’yanta.

13 Aladen jeji kuma za su tattake ta,

Namomin jeji duka za su cinye ta.

14 Ka juyo wurinmu, ya Allah Mai Runduna!

Daga Sama, ka dube mu,

Ka zo ka ceci kurangar inabinka!

15 Ka zo ka ceci kurangar inabin nan

Wadda kai da kanka ka dasa,

Wannan ƙaramar kuranga,

Ka sa ta yi girma, ta yi ƙarfi sosai!

16 Abokan gābanmu sun sa mata wuta, sun sare ta,

Ka yi fushi da su, ka hallaka su!

17 Ka kiyaye jama’arka wadda ka zaɓa,

Ka keɓe ta.

Al’umman nan wadda ka sa ta yi girma, ta yi ƙarfi sosai!

18 Ba za mu ƙara rabuwa da kai ba,

Ka rayar da mu, mu kuwa za mu yabe ka.

19 Ka komo da mu, ya Ubangiji Allah Mai Runduna!

Ka nuna mana ƙaunarka, za mu kuwa cetu!