ZAB 81

Waƙar Idi

1 Ku yi sowa ta farin ciki ga Allah Mai Cetonmu,

Ku raira yabbai ga Allah na Yakubu!

2 A fara waƙa, ku buga bandiri,

Ku yi waƙoƙi masu daɗi da molaye, da garayu.

3 Ku busa ƙaho domin idin,

A amaryar wata,

Da a tsakiyar farin wata.

4 Wannan doka ce a Isra’ila,

Umarni ne kuma daga Allah na Yakubu.

5 Ya ba da wannan umarni ga jama’ar Isra’ila,

A lokacin da ya fita gāba da ƙasar Masar.

Na ji wata murya da ban saba ji ba tana cewa,

6 “Na ɗauke muku kayayyaki masu nauyi da kuke ɗauke da su a kā,

Na sa kuka ajiye kwandunan aikinku.

7 Sa’ad da kuke shan wahala

Kuka yi kira a gare ni, na kuwa cece ku.

Daga maɓuyata cikin hadiri, na amsa muku,

Na jarraba ku a maɓuɓɓugan Meriba.

8 “Ya kuma jama’ata Isra’ila ku kasa kunne,

Ina kuwa so ku saurara gare ni.

9 Faufau kada ku bauta wa gumaka,

Ko ku yi sujada ga wanina.

10 Ni ne Ubangiji Allahnku,

Wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar.

Ku buɗe bakinku, zan ciyar da ku.

11 “Amma jama’ata ba su kasa kunne gare ni ba.

Isra’ila ta ƙi yi mini biyayya.

12 Saboda haka na bar su su yi ta kangarewarsu,

Su aikata duk irin abin da suka ga dama.

13 Ina kuwa so jama’ata su kasa kunne gare ni,

Su kuwa yi mini biyayya!

14 Da sai in kori abokan gābansu nan da nan,

In yi nasara da dukan maƙiyansu.

15 Maƙiyana, za su sunkuya a gabana saboda tsoro,

Hukuncinsu na har abada ne.

16 Zan ciyar da ku da kyakkyawar alkama,

In ƙosar da ku da zuma.”