ZAB 82

Tsautawa a kan Muguwar Shari’a

1 Allah yana matsayinsa a taron jama’arsa,

Yakan zartar da nufinsa a taron alloli.

2 Tilas ku daina yin rashin gaskiya a shari’a,

Ku daina goyon bayan mugaye!

3 Ku kāre hakkin talakawa da na marayu,

Ku yi adalci ga matalauta,

Da waɗanda ba su da mataimaki.

4 Ku kuɓutar da talakawa da matalauta,

Ku cece su daga ikon mugaye!

5 “Waɗanne irin jahilai ne ku, wawaye!

Kuna zaune cikin duhu,

Ga shi, ba adalci a duniya sam!

6 Na faɗa muku, ku alloli ne,

Cewa dukanku ‘ya’ya ne na Maɗaukaki.

7 Amma za ku mutu kamar kowane mutum,

Ku fāɗi kamar kowane basarauce.”

8 Ya Allah, ka zo, ka mallaki duniya,

Dukan al’ummai naka ne.