ZAB 83

Addu’a don A Hallaka Abokan Gāban Isra’ila

1 Ya Allah, kada ka yi shiru,

Kada ka tsaya cik,

Ya Allah, kada kuma ka yi tsit!

2 Duba, abokan gābanka suna tawaye,

Maƙiyanka sun tayar.

3 Suna ta ƙulle-ƙulle a asirce gaba da jama’arka,

Suna shirya maƙarƙashiya gāba da waɗanda kake tsaronsu.

4 Suna cewa, “Ku zo, mu hallakar da al’ummarsu,

Don a manta da Isra’ila har abada!”

5 Suka yarda a kan abin da suka shirya,

Suka haɗa kai gāba da kai.

6 Su ne mutanen Edom, da Isma’ilawa,

Da mutanen Mowab, da Hagarawa,

7 Da mutanen Gebal, da na Ammon, da na Amalek,

Da na Filistiya, da na Taya.

8 Assuriya ma ta haɗa kai da su,

Haɗa kai ke nan mai ƙarfi da zuriyar Lutu.

9 Ka yi musu yadda ka yi wa Madayanawa,

Ka yi musu yadda ka yi wa Sisera

Da Yabin a Kogin Kishon,

10 Waɗanda aka kora a Endor,

Gawawwakinsu kuwa suka ruɓe a ƙasa.

11 Ka yi wa shugabannin yaƙinsu yadda ka yi wa Oreb da Ziyib,

Ka kori dukan masu mulkinsu yadda ka kori Zeba da Zalmunna,

12 Waɗanda suka ce, “Za mu ƙwace ƙasar da take ta Allah, ta zama tamu.”

13 Ya Allahna, ka warwatsa su kamar ƙura,

Ka warwatsa su kamar ciyayin da iska take hurawa.

14 Kamar yadda wuta take cin jeji,

Kamar yadda harshen wuta yake ƙone tuddai,

15 Ka runtume su da hadirinka,

Ka razanar da su da iskarka mai ƙarfi.

16 Ya Ubangiji, ka sa kunya ta rufe su,

Don su so su bauta maka.

17 Ka sa a kore su, a razanar da su har abada,

Ka sa su mutu, mutuwar ƙasƙanci!

18 Ka sa su sani kai kaɗai ne Ubangiji,

Kai kaɗai ne mamallakin dukan duniya!