ZAB 84

Sa Zuciya ga Haikali

1 Ina ƙaunar Haikalinka ƙwarai,

Ya Allah Mai Iko Dukka!

2 A can nake so in kasance!

Ina marmarin farfajiyar Haikalin Ubangiji.

Da farin ciki mai yawa zan raira waƙa ga Allah Mai Rai.

3 Har ba’u ma sukan yi sheƙa,

Tsattsewa suna da sheƙunansu,

A kusa da bagadanka suke kiwon ‘ya’yansu.

Ya Ubangiji Maɗaukaki, Sarkina, Allahna.

4 Masu murna ne waɗanda suke zaune a Haikalinka,

Kullum suna raira yabonka!

5 Masu murna ne waɗanda suka sami ƙarfinsu daga gare ka,

Su waɗanda suka ƙosa su kai ziyara a Dutsen Sihiyona.

6 Sa’ad da suke ratsa busasshen kwari,

Sai ya zama maɓuɓɓugar ruwa,

Ruwan sama na farko yakan rufe wurin da tafkuna.

7 Sukan yi ta ƙara jin ƙarfi a cikin tafiyarsu,

Za su kuwa ga Allahn alloli a Sihiyona!

8 Ka ji addu’ata, ya Ubangiji Allah Mai Runduna,

Ka ji ni, ya Allah na Yakubu!

9 Duba, ya Allah, kai ne garkuwarmu,

Ka dubi fuskar Sarkinmu, zaɓaɓɓenka.

10 Kwana guda da za a yi a Haikalinka,

Ya fi kwana dubu da za a yi a wani wuri dabam.

Na gwammace in tsaya a ƙofar Haikalin Allahna,

Da in zauna a gidajen mugaye.

11 Ubangiji shi ne makiyayinmu, sarkinmu mai daraja,

Yakan sa mana albarka, da alheri, da daraja,

Ba ya hana kowane abu mai kyau ga waɗanda suke aikata abin da yake daidai.

12 Masu farin ciki ne waɗanda suka dogara gare ka,

Ya Allah Mai Runduna!