ZAB 85

Addu’a don Lafiyar Al’ummar

1 Ya Ubangiji, ka yi wa ƙasarka alheri,

Ka sāke arzuta Isra’ila kuma.

2 Ka gafarta wa jama’arka zunubansu,

Ka kuwa gafarta musu dukan kuskurensu,

3 Ka daina yin fushi da su,

Ka kuwa kawar da zafin fushinka.

4 Ka komo da mu, ya Allah Mai Cetonmu,

Ka daina jin haushinmu!

5 Za ka yi fushi da mu har abada?

Ba za ka taɓa hucewa ba?

6 Ka daɗa mana ƙarfi, ka yarda ka sabunta ƙarfinmu,

Mu kuwa, jama’arka, za mu yabe ka.

7 Ka ƙaunace mu da madawwamiyar ƙaunarka, ya Ubangiji,

Ka taimake mu da cetonka.

8 Ina kasa kunne ga abin da Ubangiji Allah yake cewa,

Mu da muke mutanensa, ya alkawarta mana salama,

Idan ba mu koma kan al’amuranmu na wauta ba.

9 Hakika a shirye yake yă ceci waɗanda suke girmama shi,

Kasancewarsa a ƙasar, ceto ne ga ƙasar.

10 Ƙauna da aminci za su sadu wuri ɗaya,

Adalci da salama za su gamu.

11 Amincin mutum zai yunƙura daga duniya, yă nufi sama.

Adalcin Allah kuwa zai dubo daga Sama.

12 Ubangiji zai arzuta mu,

Ƙasarmu kuwa za ta ba da amfanin gona mai yawa.

13 Adalci zai yi tafiya a gaban Ubangiji,

Yă shirya masa tafarki.