ZAB 86

Addu’ar Neman Jinƙan Allah

1 Ka kasa kunne gare ni, ya Ubangiji, ka amsa mini,

Gama ba ni da ƙarfi, ba ni kuwa da mataimaki.

2 Ka cece ni daga mutuwa, saboda ni mai aminci ne a gare ka,

Ka cece ni saboda ni bawanka ne, ina kuwa dogara gare ka.

3 Kai ne Allahna, saboda haka ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji,

Ina yin addu’a a gare ka dukan yini.

4 Ka sa bawanka yă yi murna, ya Ubangiji,

Saboda addu’o’ina sun hau zuwa gare ka.

5 Ya Ubangiji, kai managarci ne, mai yin gafara,

Cike kake da madawwamiyar ƙauna ga dukan waɗanda suke yin addu’a gare ka.

6 Ka ji addu’ata, ya Ubangiji,

Ka ji kukana na neman taimako!

7 Nakan kira gare ka a lokacin wahala,

Saboda kakan amsa addu’ata.

8 Ba wani allah kamarka, ya Ubangiji,

Ba ko ɗaya, ba wanda zai iya aikata abin da kake aikatawa.

9 Dukan sauran al’umma da ka halitta

Za su zo su rusuna har ƙasa a gabanka.

Za su yabi girmanka,

10 Gama kai kaɗai ne Maɗaukaki, ya Allah,

Kai kaɗai ne ka aikata abubuwa na banmamaki.

11 Ya Ubangiji, ka koya mini abin da kake so in yi,

Ni kuwa zan yi maka biyayya da aminci.

Ka koya mini in bauta maka da zuciya ɗaya.

12 Zan yabe ka da zuciya ɗaya, ya Ubangiji Allahna,

Zan riƙa shelar girmanka har abada.

13 Wane irin girma madawwamiyar ƙaunarka take da shi a gare ni!

Gama ka cece ni daga zurfin kabari.

14 Masu girmankai sun tasar mini, ya Allah,

Ƙungiyar mugaye tana ƙoƙari ta kashe ni,

Mutanen da ba su kula da kai ba.

15 Ya Ubangiji, kai Allah ne mai jinƙai, mai ƙauna,

Mai jinkirin fushi, kullum kai mai alheri ne, mai aminci.

16 Ka juyo gare ni, ka yi mini jinƙai,

Ka ƙarfafa ni, ka cece ni,

Gama ina bauta maka, kamar yadda mahaifiyata ta yi.

17 Ka nuna mini alherinka, ya Ubangiji,

Sa’an nan su waɗanda suke ƙina za su sha kunya,

Sa’ad da suka ga ka ta’azantar da ni,

Ka kuma taimake ni.