ZAB 87

Fa’idar Zama a Urushalima

1 Allah ya gina birninsa a bisa tsarkakan tuddai,

2 Yana ƙaunar birnin Urushalima fiye da kowane wuri a Isra’ila.

3 Ya birnin Allah, ka kasa kunne,

Ga abubuwan banmamaki da ya faɗa a kanka.

4 “Sa’ad da na lasafta sauran al’umma da suke yi mini biyayya,

Zan sa Masar da Babila a cikinsu,

Zan ce da Filistiya, da Taya, da Habasha,

Su ma na Urushalima ne.”

5 A kan Sihiyona kuwa za a ce,

“Dukan sauran al’umma nata ne.”

Maɗaukaki kuwa zai ƙarfafa ta.

6 Ubangiji zai rubuta lissafin jama’o’i,

Ya sa su duka cikin jimilla ta Urushalima.

7 Duk mazauna a wurin za su raira waƙa, su yi rawa,

Su ce, “Dukan maɓuɓɓugaina suna cikinka.”