ZAB 88

Kukan Neman Taimako

1 Ya Ubangiji Allah, Mai Cetona,

Duk yini ina ta kuka,

Da dare kuma na zo gare ka.

2 Ka ji addu’ata,

Ka kasa kunne ga kukana na neman taimako!

3 Wahala mai yawa ta auko mini,

Har ina gab da mutuwa.

4 Ina daidai da sauran mutanen da suke gab da mutuwa,

Dukan ƙarfina ya ƙare.

5 An yashe ni a cikin matattu,

Kamar waɗanda aka karkashe,

Suna kuma kwance cikin kaburburansu,

Waɗanda ka manta da su ɗungum,

Waɗanda taimakonka ya yi musu nisa.

6 Ka jefar da ni cikin zurfin kabari,

Da cikin rami mafi zurfi, mafi duhu.

7 Fushinka yana da nauyi a kaina,

An turmushe ni a cikin tuƙuƙinka.

8 Ka sa abokaina su yashe ni,

Ka sa sun ware ni.

An kange ni, ba yadda zan kuɓuta.

9 Idanuna sun raunana saboda wahala.

Ya Ubangiji, kowace rana ina kira gare ka,

Ina ta da hannuwana zuwa gare ka da addu’a!

10 Kakan yi wa matattu mu’ujizai ne?

Sukan tashi su yabe ka?

11 Akan yi maganar madawwamiyar ƙaunarka a kabari?

Ko amincinka a inda ake hallaka?

12 Za a iya ganin mu’ujizanka a cikin duhu?

Ko kuwa alherinka a lahira?

13 Ya Ubangiji, ina kira gare ka, neman taimako,

Kowace safiya nakan yi addu’a gare ka.

14 Me ya sa ka yashe ni, ya Ubangiji?

Me ya sa ka ɓoye kanka daga gare ni?

15 Tun ina ƙarami nake shan wahala,

Har ma na kusa mutuwa,

Na tafke saboda nauyin hukuncinka.

16 Hasalarka ta bi ta kaina,

Tasar mini da kake ta yi, ta hallaka ni.

17 Dukan yini sun kewaye ni kamar rigyawa,

Ta kowace fuska, sun rufe ni.

18 Ka sa har abokaina na kusa sun yashe ni,

Duhu ne kaɗai abokin zamana.