ZAB 96

Allah Maɗaukakin Sarki Ne

1 Ku raira sabuwar waƙa ga Ubangiji!

Ku raira waƙa ga Ubangiji, ya duniya duka!

2 Ku raira waƙa ga Ubangiji, ku yabe shi!

Kowace rana ku ba da labari mai daɗi cewa,

“Ya cece mu!”

3 Ku yi shelar ɗaukakar Ubangiji ga sauran al’umma,

Ku yi shelar ayyukansa masu girma ga dukan kabilai.

4 Ubangiji da girma yake, tilas a ɗaukaka shi,

Tilas a fi jin tsoronsa fiye da dukan alloli.

5 Allolin dukan al’ummai, gumaka ne kawai,

Amma Ubangiji ne ya yi sammai.

6 Daraja da ɗaukaka suna kewaye da shi,

Girma da jamali suna cikin Haikalinsa.

7 Dukan jama’ar da suke bisa duniya su yabi Ubangiji!

Ku yabi ɗaukakarsa da ikonsa!

8 Ku yabi sunan Ubangiji mai ɗaukaka,

Ku kawo sadaka, ku shiga Haikalinsa.

9 Ku durƙusa a gaban Mai Tsarki, sa’ad da ya bayyana,

Ku yi rawar jiki a gabansa, ku duniya duka!

10 A faɗa wa dukan sauran al’umma, “Ubangiji Sarki ne!

Duniya ta kahu da ƙarfi a wurin zamanta,

Ba za a iya kaushe ta ba,

Shi zai shara’anta dukan jama’a da adalci.”

11 Duniya da sararin sama, ku yi murna!

Ki yi ruri, ya ke teku da dukan masu rai da suke cikinki,

12 Ku yi murna ya ku filaye da dukan abubuwan da suke cikinku!

Sa’an nan itatuwan da suke cikin kurama

Za su ta da murya saboda farin ciki

13 A gaban Ubangiji, gama ya zo ne ya mallaki duniya.

Zai mallaki dukan jama’ar duniya

Da adalci da gaskiya.