ZAB 97

Allah Ne Mai Mulkin Dukka

1 Ubangiji Sarki ne! Ki yi murna ke duniya!

Ku yi murna, dukanku tsibiran da suke cikin tekuna!

2 Gajimare da duhu sun kewaye shi.

A kan adalci da gaskiya ya kafa mulkinsa.

3 Wuta tana tafe a gabansa, tana cinye maƙiyansa

Waɗanda suke kewaye da shi.

4 Walƙiyarsa ta haskaka duniya,

Duniya kuwa ta gani ta yi ta rawar jiki.

5 Tuddai sun narke a gaban Ubangiji kamar kākin zuma,

A gaban Ubangijin dukan duniya.

6 Sammai suna shelar adalcinsa,

Dukan kabilai kuwa, sun ga ɗaukakarsa.

7 Dukan waɗanda suke yi wa siffofi sujada za su sha kunya,

Haka kuma waɗanda suke fāriya da gumakansu.

Dukan alloli za su rusuna a gabansa.

8 Jama’ar Sihiyona suna murna,

Garuruwan Yahuza kuma suna farin ciki,

Sabili da irin shari’unka, ya Ubangiji!

9 Ya Ubangiji Mai Iko Dukka, kai kake mulkin dukan duniya,

Ka fi sauran alloli duka girma.

10 Ubangiji yana ƙaunar masu ƙin mugunta.

Yakan kiyaye rayukan jama’arsa,

Yakan cece su daga ikon mugaye.

11 Haske yakan haskaka adalai,

Haka kuma murna ta cika ga masu nagarta.

12 Dukanku adalai ku yi murna,

Saboda abin da Ubangiji ya yi!

Ku tuna da abin da Mai Tsarki ya yi,

Ku yi masa godiya!