ZAB 98

Yabo saboda Adalcin Allah

1 Ku raira sabuwar waƙa ga Ubangiji,

Gama ya aikata ayyuka masu banmamaki!

Ta wurin ikonsa, da ƙarfinsa mai tsarki ya yi nasara.

2 Ubangiji ya bayyana cin nasararsa,

Ya sanar da ikonsa na ceto ga sauran al’umma.

3 Ya cika alkawarinsa wanda ya yi wa jama’ar Isra’ila,

Da tabbatacciyar ƙauna da aminci.

Dukan mutane ko’ina sun ga nasarar Allahnmu!

4 Ku raira waƙa ta farin ciki ga Ubangiji.

Dukanku waɗanda suke a duniya,

Ku yabe shi da waƙoƙi, kuna ta da murya da ƙarfi,

Saboda farin ciki!

5 Ku raira yabbai ga Ubangiji da garayu,

Ku kaɗa garayu!

6 Ku busa kakaki da ƙahoni,

Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, Sarki!

7 Ki yi ruri, ya ke teku,

Ke da dukan masu rai waɗanda suke cikinki,

Ki raira waƙa, ke duniya,

Da dukan waɗanda suke zaune cikinki!

8 Ku yi tāfi, ya ku tekuna,

Ku raira waƙa tare, ya ku tuddai, don farin ciki.

9 A gaban Ubangiji, gama ya zo ne ya yi mulki bisa duniya!

Zai yi mulki bisa dukan jama’ar duniya da adalci da gaskiya.