ZAB 99

Amincin Allah ga Isra’ila

1 Ubangiji Sarki ne,

Mutane suna rawar jiki,

Yana zaune a bisa kursiyinsa a bisa kerubobi,

Duniya ta girgiza.

2 Ubangiji mai iko ne a Sihiyona,

Shi ne yake mulki a bisa dukan sauran al’umma.

3 Kowa da kowa zai yabi sunansa mai girma, Maɗaukaki,

Mai Tsarki ne shi!

4 Maɗaukaki kana ƙaunar abin da yake daidai,

Ka kawo adalci cikin Isra’ila,

Ka kawo adalci da gaskiya.

5 Ku yabi Ubangiji Allahnmu,

Ku yi sujada a gaban kursiyinsa!

Mai Tsarki ne shi!

6 Musa da Haruna firistocinsa ne,

Sama’ila kuma mai yi masa sujada ne.

Suka yi kira ga Ubangiji, ya kuwa amsa musu.

7 Ya yi magana da su daga girgije,

Suka yi biyayya da dokoki da umarnai da ya ba su.

8 Ya Ubangiji Allahnmu, ka amsa wa jama’arka,

Ka nuna musu, kai Allah ne mai yin gafara,

Amma kakan hukunta su saboda zunubansu.

9 Ku yabi Ubangiji Allahnmu,

Ku yi sujada a bisa dutsensa mai tsarki!

Ubangiji Allahnmu Mai Tsarki ne!