ZAB 100

Waƙar Yabo

1 Bari dukan duniya ta raira waƙar farin ciki ga Ubangiji!

2 Ku yi wa Ubangiji sujada da murna,

Ku zo gabansa, kuna raira waƙoƙin farin ciki!

3 Kada fa a manta da cewa, Ubangiji shi ne Allah!

Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne,

Mu jama’arsa ne, mu garkensa ne.

4 Ku shiga Haikalinsa da godiya,

Ku shiga wurinsa mai tsarki, ku yabe shi!

Ku gode masa, ku yabe shi!

5 Ubangiji nagari ne,

Ƙaunarsa madawwamiya ce,

Amincinsa kuwa har abada abadin ne.