1 SAM 7

1 Mutanen Kiriyat-yeyarim kuwa suka zo suka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji suka kai shi gidan Abinadab a bisa tudu. Suka keɓe ɗansa, Ele’azara, ya lura da akwatin alkawarin Ubangiji.

Sama’ila Ya Shugabanci Isra’ila

2 Akwatin alkawarin Ubangiji ya daɗe a Kiriyat-yeyarim, ya kai har shekara ashirin. A wannan lokaci kuwa dukan Isra’ilawa suka yi kuka ga Ubangiji domin ya taimake su.

3 Sa’an nan Sama’ila ya ce wa mutanen Isra’ila, “Idan da zuciya ɗaya kuke komowa wurin Ubangiji, to, sai ku rabu da baƙin alloli, da gumakan nan Ashtarot. Ku sa zuciyarku ga bin Ubangiji, ku bauta masa shi kaɗai, shi kuwa zai cece ku daga hannun Filistiyawa.”

4 Isra’ilawa kuwa suka rabu da gumakan Ba’al da Ashtarot, suka bauta wa Ubangiji shi kaɗai.

5 Sama’ila kuma ya ce, “Ku tattara dukan Isra’ilawa a Mizfa, ni kuwa zan yi addu’a ga Ubangiji dominku.”

6 Isra’ilawa fa suka taru a Mizfa, suka kawo ruwa, suka zuba a gaban Ubangiji. Suka yi azumi a ranan nan, suka ce, “Mun yi wa Ubangiji zunubi.” Sama’ila kuwa ya zauna a Mizfa ya yi mulkin Isra’ilawa.

7 Da Filistiyawa suka ji Isra’ilawa sun taru a Mizfa, sai sarakunan Filistiyawa, su biyar, suka tafi, su yi yaƙi da Isra’ilawa. Sa’ad da Isra’ilawa suka ji labari, sai suka tsorata,

8 suka ce wa Sama’ila, “Ka yi ta roƙo ga Ubangiji Allahnmu don ya cece mu daga hannun Filistiyawa.”

9 Sama’ila ya kama ɗan rago ya miƙa shi ɗungum hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Ya kuma yi roƙo ga Ubangiji ya taimaki Isra’ilawa, Ubangiji kuwa ya amsa addu’arsa.

10 A sa’ad da Sama’ila yake miƙa hadaya ta ƙonawa, Filistiyawa suka matso don su yi yaƙi da Isra’ilawa, sai Ubangiji ya buge wa Filistiyawa tsawa mai ƙarfi daga sama, suka kuwa ruɗe suka juya a guje.

11 Isra’ilawa suka fito daga Mizfa suka runtumi Filistiyawa, suka yi ta karkashe su har zuwa kwarin Bet-kar.

12 Sa’an nan Sama’ila ya ɗauki dutse ya kafa shi a tsakanin Mizfa da Shen, ya sa masa suna, Ebenezer, wato “Har wa yau Ubangiji yana taimakonmu.”

13 Ta haka aka ci Filistiyawa. Daga nan ba su ƙara shiga yankin ƙasar Isra’ilawa ba, gama Ubangiji ya yi gāba da Filistiyawa a dukan zamanin Sama’ila.

14 Aka mayar wa Isra’ilawa garuruwan da Filistiyawa suka ƙwace musu, tun daga Ekron har zuwa Gat. Isra’ilawa kuma suka ƙwato dukan yankin ƙasarsu daga hannun Filistiyawa. Akwai kuma zaman lafiya tsakanin Isra’ilawa da Ƙan’aniyawa.

15 Sama’ila kuwa ya yi mulkin Isra’ilawa dukan kwanakin ransa.

16 A kowace shekara yakan fita rangadi zuwa Betel, da Gilgal, da Mizfa, inda yakan yi musu shari’a.

17 Sa’an nan kuma ya koma gidansa a Rama inda kuma yakan yi wa Isra’ilawa shari’a. Ya kuma gina wa Ubangiji bagade a can Rama.