1 SAM 8

Isra’ilawa Sun Roƙa A Naɗa musu Sarki

1 Da Sama’ila ya tsufa, sai ya naɗa ‘ya’yansa maza su zama alƙalan Isra’ila.

2 Sunan ɗansa na fari Yowel, na biyun kuma Abaija. Su ne alƙalai a cikin Biyer-sheba.

3 Amma ‘ya’yansa ba su bi gurbin mahaifinsu ba, amma suka mai da hankalinsu ga neman kuɗi, suka yi ta cin hanci, suka danne gaskiya.

4 Dukan shugabannin Isra’ila kuwa suka tattaru, suka tafi wurin Sama’ila a Rama,

5 suka ce masa, “Ga shi, ka tsufa, ga kuma ‘ya’yanka ba su bi gurbinka ba, yanzu dai sai ka naɗa mana sarki wanda zai yi mulkinmu kamar sauran ƙasashe.”

6 Amma Sama’ila bai ji daɗin roƙonsu ba, na a naɗa musu sarki, saboda haka ya yi addu’a ga Ubangiji.

7 Ubangiji kuwa ya ce masa, “Sai ka kasa kunne ga dukan abin da suka faɗa maka, gama ba kai suka ƙi ba, amma ni suka ƙi da zama sarkinsu.

8 Irin abubuwan da suke yi maka, irinsu ne suka yi mini tun daga ranar da na fito da su daga Masar har wa yau, sun ƙi ni, suka yi ta bauta wa gumaka.

9 Yanzu dai sai ka saurari maganarsu kurum, amma ka faɗakar da su sosai da sosai, ka kuma nuna musu irin halin sarkin da zai sarauce su.”

10 Sama’ila kuwa ya faɗa wa mutanen da suke roƙo ya naɗa musu sarki dukan abin da Ubangiji ya faɗa.

11 Ya ce musu, “Ga irin halin sarkin da zai sarauce ku, zai sa ‘ya’yanku maza su zama sojojinsa, waɗansunsu za su yi aiki da karusan yaƙinsa, waɗansu su zama mahayan dawakansa, da masu kai hari musamman.

12 Waɗansu kuma zai sa su zama shugabannin mutum dubu dubu da na hamsin hamsin. ‘Ya’yanku ne za su riƙa yi masa noma da girbi, su ƙera masa kayayyakin yaƙi da na karusansa.

13 Zai sa ‘ya’yanku mata yin aikin turare, da dafe-dafe, da toye-toye.

14 Zai ƙwace gonakinku mafi kyau, da gonakinku na inabi, da gonakinku na zaitun, ya ba fādawansa.

15 Zai kuma karɓi ushirin hatsinku da na inabinku ya ba shugabannin fādarsa da sauran fādawansa.

16 Zai ƙwace bayinku mata da maza, da mafi kyau na shanunku da jakunanku, domin su riƙa yi masa aiki.

17 Zai kuma karɓi ushirin dabbobinku. Za ku zama barorinsa.

18 A lokacin za ku yi kuka saboda sarkin da kuka zaɓar wa kanku, amma Ubangiji ba zai kasa kunne ga kukanku ba.”

19 Amma mutane suka ƙi jin abin da Sama’ila ya faɗa musu, sai suka ce, “Duk da haka dai, muna so sarki ya sarauce mu,

20 don mu ma mu zama kamar sauran ƙasashe, mu sami sarki wanda zai sarauce mu, ya shugabance mu zuwa yaƙe-yaƙe.”

21 Sa’ad da Sama’ila ya ji dukan abin da mutanen suka faɗa, sai ya mayar wa Ubangiji.

22 Ubangiji kuwa ya ce wa Sama’ila, “Ka yarda da abin da suka ce, ka naɗa musu sarki.”

Sai Sama’ila ya ce wa mutanen Isra’ila, “Kowa ya koma gida.”