AYU 11

Zofar Ya Zargi Ayuba a kan Aikata Laifi

1 Zofar ya amsa.

2 “Ba wanda zai amsa dukan wannan surutu?

Yawan magana yakan sa mutum ya zama daidai?

3 Ayuba,kana tsammani ba za mu iya ba ka amsa ba?

Kana tsammani maganganunka na ba’a

Za su sa mu rasa abin da za mu mayar maka?

4 Ka ɗauka duk abin da kake faɗa gaskiya ne,

Ka kuma mai da kanka kai mai tsarki ne a gaban Allah.

5 Da ma Allah zai amsa maka,

Ya yi magana gāba da kai,

6 Da ya faɗa maka hikima tana da fannoni da yawa.

Akwai abubuwa waɗanda suka fi ƙarfin ganewar ɗan adam.

Duba, Allah ya ƙyale wani ɓangare na laifinka.

7 “Kana iya gane matuƙa da iyakar

Girman Allah da na ikonsa?

8 Sararin sama ba shi ne matuƙa a wurin Allah ba,

Amma ga shi, yana can nesa da kai,

Allah ya san lahira,

Amma kai ba ka sani ba.

9 Fāɗin girman Allah ya fi duniya

Ya kuma fi teku fāɗi.

10 Idan Allah ya kama ka ya gurfanar da kai gaban shari’a,

Wa zai iya hana shi?

11 Allah ya san irin mutanen da ba su da amfani,

Domin yana ganin dukan mugayen ayyukansu.

12 Idan dakikan mutane sa yi hikima,

To, jakunan jeji ma sa yi irin hali na gida.

13 “Ayuba, ka shirya zuciyarka,

Ka ɗaga hannuwanka zuwa wurin Allah.

14 Ka kawar da mugunta da kuskure daga gidanka.

15 Sa’an nan ka sāke shan ɗamarar zaman duniya,

Da ƙarfi da rashin tsoro.

16 Duk wahalarka za ta gushe daga tunaninka,

Kamar yadda rigyawa takan wuce, ba a ƙara tunawa da ita.

17 Ranka zai yi haske fiye da hasken rana da tsakar rana.

Kwanakin ranka mafiya duhu

Za su yi haske kamar ketowar alfijir.

18 Za ka yi zaman lafiya, cike da sa zuciya,

Allah zai kiyaye ka, ya ba ka hutawa.

19 Ba za ka ji tsoron kowane maƙiyi ba,

Mutane da yawa za su nemi taimako daga gare ka.

20 Amma mugaye za su dudduba ko’ina da fid da zuciya,

Ba su da wata hanyar da za su kuɓuta.

Sauraronsu kaɗai shi ne mutuwa.”