FIT 2

Haihuwar Musa

1 Sai wani mutum, Balawe, ya auro ‘yar Lawi.

2 Matar kuwa ta yi ciki, ta haifi ɗa. Sa’ad da ta ga jaririn kyakkyawa ne, sai ta ɓoye shi har wata uku.

3 Da ta ga ba za ta iya ƙara ɓoye shi ba, sai ta saƙa kwando da iwa, ta yaɓe shi da katsi, ta sa jaririn a ciki, ta ajiye shi cikin kyauro a bakin Kogin Nilu.

4 Ga ‘yar’uwarsa kuma a tsaye daga nesa don ta san abin da zai same shi.

5 Gimbiya, wato ‘yar Fir’auna, ta gangaro domin ta yi wanka a Kogin Nilu, barorinta ‘yan mata suna biye da ita a gaɓar Kogin Nilu. Da ta ga kwando a cikin kyauro, ta aiki baranyarta ta ɗauko mata shi.

6 Sa’ad da ta tuɗe kwandon ta ga jariri yana kuka. Sai ta ji tausayinsa, ta ce, “Wannan ɗaya daga cikin ‘ya’yan Ibraniyawa ne.”

7 ‘Yar’uwar jaririn kuwa ta ce wa Gimbiya, “In tafi in kirawo miki wata daga cikin matan Ibraniyawa da za ta yi miki renon ɗan?”

8 Sai Gimbiya ta ce mata, “Je ki.” Yarinyar kuwa ta tafi ta kirawo mahaifiyar jaririn.

9 Da ta zo, sai Gimbiya ta ce mata, “Dauki wannan jariri, ki yi mini renonsa, zan biya ki ladanki.” Matar kuwa ta ɗauki jaririn ta yi renonsa.

10 Da jaririn ya yi girma sai ta kai shi wurin Gimbiyar. Yaro kuwa ya zama tallafinta. Ta raɗa masa suna Musa, gama ta ce, “Domin na tsamo shi daga cikin ruwa.”

Musa Ya Gudu zuwa Madayana

11 Ana nan wata rana, sa’ad da Musa ya yi girma, ya tafi wurin mutanensa, sai ya ga yadda suke shan wahala. Ya kuma ga wani Bamasare yana dūkan Ba’ibrane, ɗaya daga cikin ‘yan’uwansa.

12 Da ya waiwaya, bai ga kowa ba, sai ya kashe Bamasaren, ya turbuɗe shi cikin yashi.

13 Kashegari da ya sāke fita, sai ya ga waɗansu Ibraniyawa biyu suna faɗa da juna. Ya ce wa wanda yake ƙwaran ɗan’uwansa, “Me ya sa kake bugun ɗan’uwanka?”

14 Ya amsa, ya ce, “Wa ya naɗa ka sarki ko alƙali a bisanmu? So kake ka kashe ni kamar yadda ka kashe Bamasaren?”

Sai Musa ya tsorata, ya ce, “Assha, ashe, an san al’amarin!”

15 Da Fir’auna ya ji, sai ya nema ya kashe Musa. Amma Musa ya gudu daga gaban Fir’auna, ya tafi, ya zauna a ƙasar Madayana. Da ya kai, sai ya zauna a bakin wata rijiya.

16 Ana nan waɗansu ‘yan mata bakwai, ‘ya’yan firist na Madayana suka zo su cika komaye da ruwa domin su shayar da garken mahaifinsu.

17 Sai makiyaya suka zo, suka kore su, amma Musa ya tashi ya taimake su, ya kuma shayar da garkensu.

18 Lokacin da suka koma wurin mahaifinsu, Reyuwel, wato Yetro, ya ce musu, “Yaya aka yi yau, kuka komo da sauri haka?”

19 Sai suka ce, “Wani Bamasare ne ya cece mu daga hannun makiyaya, har ya ɗebo ruwa, ya shayar da garkenmu.”

20 Reyuwel kuwa ya ce wa ‘ya’yansa mata, “A ina yake? Me ya sa ba ku zo da shi ba? Ku kirawo shi, ya zo, ya ci abinci.”

21 Musa kuwa ya yarda ya zauna tare da Reyuwel. Sai ya aurar wa Musa da ‘yarsa Ziffora.

22 Ita kuwa ta haifa masa ɗa, ya raɗa masa suna Gershom, gama ya ce, “Baƙo ne ni, a baƙuwar ƙasa.”

23 Ana nan, a kwana a tashi, sai Sarkin Masar ya rasu. Jama’ar Isra’ila suka yi nishi, suka yi kuka kuma saboda bautarsu, kukansu na neman gudunmawa ya kai gun Allah.

24 Allah kuwa ya ji nishinsu, sai ya tuna da alkawarinsa da ya yi wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.

25 Allah ya dubi jama’ar Isra’ila, ya kuwa kula da su.