FIT 3

Allah a Kira Musa

1 Wata rana, sa’ad da Musa yake kiwon garken surukinsa, Yetro, firist na Madayana, sai ya kai garken yammacin jeji, har ya zo Horeb, wato dutsen Allah.

2 A can mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare shi cikin harshen wuta daga cikin kurmi. Da Musa ya duba, sai ga kurmin yana cin wuta, amma duk da haka bai ƙone ba.

3 Musa kuwa ya ce, “Bari in ratse, in ga wannan abin banmamaki da ya sa kurmin bai ƙone ba.”

4 Sa’ad da Ubangiji ya ga ya ratse don ya duba, sai Allah ya kira shi daga cikin kurmin, ya ce, “Musa, Musa.”

Musa ya ce, “Ga ni.”

5 Allah kuwa ya ce, “Kada ka matso kusa, ka cire takalminka, gama wurin da kake tsaye, tsattsarka ne.”

6 Ya kuma ce, “Ni ne Allah na kakanninka, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.” Sai Musa ya ɓoye fuskarsa, gama yana jin tsoro ya dubi Allah.

7 Ubangiji kuwa ya ce, “Na ga wahalar jama’ata waɗanda suke a Masar, na kuma ji kukansu da suke yi a kan shugabanninsu. Na san wahalarsu,

8 don haka na sauko in cece su daga hannun Masarawa, in fito da su daga cikin wannan ƙasa zuwa kyakkyawar ƙasa mai ba da yalwar abinci, wato ƙasar Kan’aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa.

9 Yanzu fa, ga shi, kukan jama’ar Isra’ila ya zo gare ni. Na kuma ga wahalar da Masarawa suke ba su.

10 Zo, in aike ka wurin Fir’auna domin ka fito da jama’ata, wato Isra’ilawa, daga cikin Masar.”

11 Amma Musa ya ce wa Allah, “Wane ni in tafi gaban Fir’auna in fito da Isra’ilawa daga cikin Masar?”

12 Sai Allah ya ce, “Zan kasance tare da kai, wannan kuwa zai zama alama a gare ka, cewa ni ne na aike ka. Sa’ad da ka fito da jama’ar daga Masar, za ku bauta wa Allah a bisa dutsen nan.”

13 Sai Musa ya ce wa Allah, “Idan na je wurin Isra’ilawa na ce musu, ‘Allah na ubanninku ya aiko ni gare ku,’ idan sun ce mini, ‘Yaya sunansa?’ Me zan faɗa musu?”

14 Allah kuwa ya ce wa Musa, “NI INA NAN YADDA NAKE,” ya kuma ce, “Haka za ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘NI NE ya aiko ni gare ku.”’

15 Allah kuma ya sāke ce wa Musa, “Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘Ubangiji Allah na kakanninku, wato na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu ya aiko ni gare ku.’ Wannan shi ne sunana har abada. Da wannan suna za a tuna da ni a dukkan zamanai.

16 Tafi, ka tattara dattawan Isra’ila, ka faɗa musu, ‘Ubangiji Allah na kakanninku ya bayyana gare ni, wato na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, ya ce, sosai ya ziyarce ku, ya kuma ga abin da ake yi muku a Masar.

17 Ya yi alkawari cewa zai fisshe ku daga wahalar Masar zuwa ƙasar Kan’aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa. Ƙasa wadda take mai ba da yalwar abinci.’

18 Za su kasa kunne ga muryarka. Sa’an nan kai da dattawan Isra’ila za ku tafi gaban Sarkin Masar ku ce masa, ‘Ubangiji Allah na Ibraniyawa ya gamu da mu. Yanzu fa, muna roƙonka, ka yarda mana mu yi tafiyar kwana uku a cikin jeji mu miƙa masa hadaya.’

19 Amma na sani Sarkin Masar ba zai bar ku ku fita ba, sai an yi masa tilas.

20 Domin haka zan miƙa hannuna in bugi Masar da dukan mu’ujizaina waɗanda zan aikata cikinta, sa’an nan zai bar ku ku fita.

21 “Zan sa wannan jama’a su yi farin jini a idanun Masarawa, sa’ad da kuka fita kuma, ba za ku fita hannu wofi ba.

22 Amma kowace mace za ta roƙi maƙwabciyarta da wadda take cikin gidanta kayan ado na azurfa, da na zinariya, da tufafi, za ku sa wa ‘ya’yanku mata da maza. Da haka za ku washe Masarawa.”