ZAB 13

Addu’ar Neman Taimako daga Wahala

1 Har yaushe za ka manta da ni, ya Ubangiji?

Har abada ne?

Har yaushe za ka ɓoye mini fuskarka?

2 Har yaushe raina zai jure da shan wahala?

Har yaushe zan yi ta ɓacin rai dare da rana?

Har yaushe maƙiyana za su riƙa cin nasara a kaina?

3 Ka dube ni, ya Ubangiji Allahna, ka amsa mini,

Ka mayar mini da ƙarfina, don kada in mutu.

4 Sa’an nan maƙiyana ba za su ce, “Ai, mun yi nasara da shi” ba!

Ba za su iya yin murna saboda fāɗuwata ba.

5 Amma ina dogara ga madawwamiyar ƙaunarka,

Zan yi murna gama za ka cece ni.

6 Zan raira waƙa ga Ubangiji,

Gama ya kyautata mini.