ZAB 14

Muguntar ‘Yan Adam da Wautarsu

1 Wawaye sukan ce wa kansu, “Ba Allah!”

Dukansu sun lalace, sun aikata mugayen al’amura,

Ba wanda yake aikata abin da yake daidai.

2 Daga Sama Ubangiji ya dubi mutane,

Yă ga ko da akwai masu hikima

Waɗanda suke yi masa sujada.

3 Amma dukansu sun koma baya,

Su duka mugaye ne,

Ba wanda yake aikata abin da yake daidai,

Babu ko ɗaya.

4 Ubangiji ya ce, “Ba su sani ba?

Duk waɗannan masu aikin mugunta jahilai ne?

Ta wurin yi wa jama’ata fashi suke zaman gari,

Ba su yin addu’a gare ni.”

5 Amma za su razana,

Gama Allah yana tare da masu yi masa biyayya.

6 Suna yi wa shirye-shiryen kāsasshe dariya,

Saboda yana dogara ga Ubangiji.

7 Ina addu’a matuƙa domin ceto ya zo ga Isra’ila daga Sihiyona!

Sa’ad da Ubangiji ya sāke arzuta jama’arsa,

Zuriyar Yakubu za su yi farin ciki,

Jama’ar Isra’ila za su yi murna.