ZAB 15

Mazauna a Tudun Allah Mai Tsarki

1 Wane ne zai iya zama cikin Haikalinka?

Wa zai iya tsayawa a Sihiyona, wato tudunka tsattsarka?

2 Sai dai mutumin da yake biyayya ga Allah da kowane abu,

Yana kuwa aikata abin da yake daidai,

Wanda yake faɗar gaskiya da zuciya ɗaya,

3 Wanda kuma ba ya ɓāta sunan waɗansu.

Ba ya zargin abokansa,

Ba ya kuwa baza jita-jita a kan maƙwabtansa.

4 Yakan raina waɗanda Allah ya ƙi su,

Amma yana girmama waɗanda suke yi wa Ubangiji biyayya,

Kullum yana cika alkawaran da ya yi ko ta halin ƙaƙa,

5 Yana ba da rance ba ruwa,

Ba ya karɓar hanci don ya yi shaidar zur a kan marar laifi.

Wanda ya aikata waɗannan abubuwa ba zai taɓa fāɗuwa ba.