ZAB 16

Gādon Alheri

1 Ya Allah, ka kiyaye ni, gama na zo gare ka neman mafaka.

2 Na ce wa Ubangiji, “Kai ne Ubangijina,

Dukan kyawawan abubuwan da nake da su

Daga gare ka suke.”

3 Dubi irin martabar da amintattun jama’ar Ubangiji suke da ita!

Ba abin da raina ya fi so,

Sai in zauna tare da su.

4 Waɗanda suke hanzari zuwa ga gumaka,

Za su jawo wa kansu wahala.

Ba zan yi tarayya da su da hadayarsu ba.

Ba zan yi sujada ga gumakansu ba.

5 Kai ne kaɗai, nake da shi, ya Ubangiji,

Kai ne kake biyan dukan bukatata,

Raina yana hannunka.

6 Kyautanka zuwa gare ni da bansha’awa suke,

Kyawawa ne kuwa ƙwarai!

7 Na yabi Ubangiji saboda yana bi da ni,

Da dare kuma lamirina yana yi mini fadaka.

8 A kullum ina jin Ubangiji yana tare da ni,

Yana nan kusa, ba abin da zai girgiza ni.

9 Don haka cike nake da murna da farin ciki,

Kullum kuwa ina jin kome lafiya yake,

10 Saboda ba za ka yarda in shiga lahira ba,

Ba za ka bar wanda kake ƙauna a zurfafa daga ƙarƙas ba.

11 Za ka nuna mini hanyar rai,

Kasancewarka takan sa in cika da farin ciki,

Taimakonka kuwa yana kawo jin daɗi har abada.