ZAB 4

Addu’ar Maraice ta Dogara ga Allah

1 Ka amsa mini sa’ad da na yi kira,

Ya Allah, madogarata!

Lokacin da nake shan wahala, ka zama mai taimakona.

Ka yi mini alheri, ka kuma saurari addu’ata!

2 Ku mutanen nan, sai yaushe za ku daina zagina?

Sai yaushe za ku daina ƙaunar abubuwan banza,

Da bin abin da yake na ƙarya?

3 Ku tuna fa, Ubangiji ne ya zaɓe ni domin in zama nasa,

Ya kuma ji ni lokacin da na yi kira gare shi.

4 Ku ji tsoro, ku daina aikata zunubinku,

Ku yi tunani da gaske a kan wannan

A kaɗaice, shiru, a ɗakunanku.

5 Ku miƙa wa Ubangiji hadayun da suka dace,

Ku kuma dogara gare shi.

6 Akwai mutane da yawa da suke cewa,

“Da ma a sa mana albarka!”

Ka dube mu da alheri, ya Ubangiji!

7 Farin cikin da ka ba ni mai yawa ne,

Fiye da na waɗanda suke da wadataccen hatsi da ruwan inabi.

8 Da zarar na kwanta, sai barci ya kwashe ni,

Kai kaɗai kake kiyaye ni sosai, ya Ubangiji.