ZAB 3

Addu’ar Safe ta Dogara ga Allah

1 Ina da maƙiya da yawa, ya Ubangiji,

Da yawa kuma sun juya, suna gāba da ni!

2 Suna magana a kaina, suna cewa,

“Allah ba zai taimake shi ba!”

3 Amma kai, ya Ubangiji, kullum kana kiyaye ni daga hatsari,

Kana ba ni nasara,

Kana kuma maido mini da ƙarfin halina.

4 Na yi kira wurin Ubangiji domin taimako,

Ya kuwa amsa mini daga tsattsarkan dutsensa.

5 Na kwanta na yi barci,

Na kuwa tashi lafiya lau,

Gama Ubangiji yana kiyaye ni.

6 Ba na jin tsoron dubban abokan gāba

Waɗanda suka kewaye ni ta kowane gefe.

7 Ka zo, ya Ubangiji! Ka cece ni, ya Allahna!

Ka yi nasara a kan dukan abokan gābana,

Ka hallakar da dukan mugaye.

8 Ceto yana zuwa daga wurin Ubangiji,

Bari yă sa wa jama’arsa albarka!