ZAB 2

Mulkin Sarkin da Ubangiji Ya Zaɓa

1 Don me al’ummai suke shirin tayarwa?

Don me waɗannan mutane suke ƙulla shawarwarin banza?

2 Sarakunan duniya sun yi tayarwa,

Masu mulkinsu suna shirya maƙarƙashiya tare,

Gāba da Ubangiji da zaɓaɓɓen sarkinsa.

3 Suna cewa, “Bari mu ‘yantar da kanmu daga mulkinsu,

Bari mu fice daga ƙarƙashinsu!”

4 Ubangiji ya yi dariya daga kan kursiyinsa can Sama,

Ya mai da su abin dariya.

5 Ya yi musu magana da fushi,

Ya razanar da su da hasalarsa,

6 Ya ce, “A bisa Sihiyona, dutsena tsattsarka,

Na naɗa sarkina.”

7 Sarkin ya ce, “Zan yi shelar abin da Ubangiji ya hurta.

Ubangiji ya ce mini, ‘Kai ɗana ne,

Yau ne na zama mahaifinka.

8 Ka yi roƙo, zan kuwa ba ka dukan al’ummai,

Dukan duniya kuma za ta zama taka.

9 Za ka mallake su da sandan ƙarfe,

Za ka farfashe su kamar tukunyar yumɓu.’ ”

10 Yanzu ku kasa kunne gare ni, ku sarakuna,

Ku mai da hankali, ku mahukunta!

11 Ku bauta wa Ubangiji da tsoro,

Ku yi rawar jiki, ku rusuna masa,

12 Ku yi mubaya’a da Ɗan,

Idan kuwa ba haka ba zai yi fushi da ku, za ku kuwa mutu,

Gama yakan yi fushi da sauri.

Albarka ta tabbata ga dukan masu zuwa gare shi neman mafaka!