ZAB 121

Ubangiji Ne Yake Kiyaye Ku

1 Na duba wajen duwatsu,

Daga ina taimakona zai zo?

2 Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji,

Wanda ya yi sama da ƙasa.

3 Ba zai bar ka ka fāɗi ba,

Makiyayinka, ba zai yi barci ba!

4 Makiyayin Isra’ila,

Ba ya gyangyaɗi ko barci!

5 Ubangiji zai lura da kai,

Yana kusa da kai domin ya kiyaye ka.

6 Ba za ka sha rana ba,

Ko farin wata da dare.

7 Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan hatsari,

Zai sa ka zauna lafiya.

8 Zai kiyaye shigarka da fitarka,

Tun daga yanzu har abada.