ZAF 3

Zunubin Urushalima da Fansarta

1 Taka ta ƙare, kai mai tayarwa,

Ƙazantaccen birni mai zalunci!

2 Ba ya kasa kunne ga muryar kowa,

Ba ya karɓar horo.

Bai dogara ga Ubangiji ba,

Bai kuma kusaci Allahnsa ba.

3 Shugabanninsa zakoki ne masu ruri,

Alƙalansa kuma kyarketai ne da sukan fito da maraice,

Waɗanda ba su rage kome kafin wayewar gari.

4 Annabawansa sakarkari ne, maciya amana.

Firistocinsa sun ƙazantar da abin da yake mai tsarki.

Sun kuma keta dokoki.

5 Ubangiji wanda yake cikinsa mai adalci ne,

Ba ya kuskure.

Yakan nuna adalcinsa kowace safiya,

Kowace safiya kuwa bai taɓa fāsawa ba.

Amma mugu bai san kunya ba.

6 Ubangiji ya ce,

“Na datse al’umman duniya,

Hasumiyansu sun lalace.

Na kuma lalatar da hanyoyinsu,

Ba mai tafiya a kansu.

An mai da biranensu kufai,

Ba mutumin da yake zaune ciki.

7 Na ce, hakika za ka ji tsorona,

Ka kuma karɓi horo.

Ba za a rushe wurin zamanta ba

Bisa ga hukuncin da na yi mata.

Amma suka ɗokanta su lalatar da ayyukansu.

8 “Domin haka ni Ubangiji na ce,

Ku jira ni zuwa ranar da zan tashi in yi tuhuma.

Gama na ƙudura zan tattara al’umman duniya, da mulkoki,

Don in kwarara musu hasalata

Da zafin fushina,

Gama zafin kishina

Zai ƙone dukan duniya.

9 “Sa’an nan zan sauye harshen mutane da harshe mai tsabta,

Domin dukansu su yi kira ga sunan Ubangiji,

Su kuma bauta masa da zuciya ɗaya.

10 Gama daga hayin kogunan Habasha,

Masu yi mini sujada,

Mutanena da yake warwatse,

Za su kawo mini hadaya.

11 A wannan rana ba za a kunyatar da kai ba,

Saboda tayarwar da ka yi mini ta wurin ayyukanka.

Gama a sa’an nan zan fitar da masu girmankai

Da masu fankama daga cikinka,

Ba za ka ƙara yin alfarma ba

A dutsena tsattsarka.

12 Zan kuwa bar mutane masu tawali’u,

Da masu ladabi a cikinka,

Su kuwa za su nemi mafaka a wurin Ubangiji.

13 Waɗanda suka ragu cikin Isra’ila,

Ba za su aikata mugunta ba,

Ba kuma za su faɗi ƙarya ba,

Gama harshen ƙarya ba zai kasance a bakinsu ba.

Za su yi kiwo, su kwanta,

Ba wanda zai tsorata su.”

Waƙar Murna

14 Ki raira waƙa da ƙarfi, ya ke Sihiyona!

Ki ta da murya, ya Isra’ila!

Ki yi murna, ki yi farin ciki,

Ya ke Urushalima!

15 Ubangiji ya kawar miki da hukuncinsa,

Ya kuma kori abokan gābanki.

Ubangiji Sarkin Isra’ila, yana a tsakiyarki,

Ba za ki ji tsoro ba.

16 A wannan rana za a ce wa Urushalima,

“Kada ki ji tsoro, ke Sihiyona,

Kada ki bar hannuwanki su raunana.

17 Ubangiji Allahnki yana tsakiyarki,

Mayaƙi mai cin nasara ne.

Zai yi murna, ya yi farin ciki da ke.

Zai sabunta ki da ƙaunarsa.

Zai kuma yi murna da ke ta wurin raira waƙa da ƙarfi.

18 Zan tara waɗanda suka yi makoki domin idi,

Waɗanda suke tare da ke,

Wato waɗanda nawayar zaman talala

Ta zamar musu abin zargi.

19 Ga shi kuwa, a wannan lokaci

Zan hukunta masu zaluntarki,

Zan kuma ceci gurgu,

Zan tattara korarru,

Zan mai da kunyarsu ta zama yabo,

Za su yi suna a duniya duka.

20 A wannan lokaci zan komo da ku gida,

In tattara ku wuri ɗaya.

Zan sa ku yi suna,

Ku sami yabo a wurin mutanen duniya duka,

A sa’ad da na mayar muku da arzikinku,

Ni Ubangiji na faɗa.”