MAK 1

Baƙin Cikin Sihiyona

1 Urushalima wadda take cike da mutane a dā,

Yanzu tana zaman kaɗaici!

Tana zama kamar mace wadda mijinta ya rasu,

Ita wadda dā ta zama babba a cikin sauran al’ummai!

Ita wadda take a dā sarauniya a cikin larduna,

Ta zama mai biyan gandu!

2 Da dare tana kuka mai zafi,

Hawaye suna zuba sharaf-sharaf a kumatunta.

Dukan masoyanta ba wanda yake ta’azantar da ita.

Dukan abokanta sun ci amanarta, sun zama maƙiyanta.

3 Yahuza ta tafi bauta tana shan azaba,

Da bauta mai tsanani.

Tana zaune a tsakiyar sauran al’umma,

Amma ba ta sami hutawa ba,

Gama masu runtumarta sun ci mata, ba hanyar tsira.

4 Hanyoyin Sihiyona suna baƙin ciki

Domin ba mai halartar ƙayyadaddun idodi.

Dukan ƙofofinta sun zama kufai,

Firistocinta suna nishi,

Budurwanta kuma suna wahala,

Ita kanta ma tana shan wuya ƙwarai.

5 Maƙiyanta sun zama shugabanninta,

Abokan gābanta kuma sun zama iyayengijinta.

Gama Ubangiji ne ya sa ta sha wahala

Saboda yawan zunubanta.

‘Ya’yanta sun tafi bauta wurin maƙiyanta.

6 Dukan darajar Sihiyona ta rabu da ita,

Shugabanninta sun zama kamar bareyin

Da ba su sami wurin kiwo ba,

Suna gudu ba ƙarfi a gaban wanda yake korarsu.

7 A kwanakin wahalarta na rashin wurin zama,

Urushalima ta tuna da dukan abubuwanta masu daraja a dā.

A lokacin da mutanenta suka fāɗa a hannun maƙiyi,

Ba wanda ya taimake ta,

Maƙiyanta sun gan ta,

Sun yi mata ba’a saboda fāɗuwarta.

8 Urushalima ta yi zunubi ƙwarai da gaske,

Saboda haka ta ƙazantu,

Dukan waɗanda suka girmama ta sun raina ta

Domin sun ga tsiraicinta,

Ita kanta ma tana nishi, ta ba da baya.

9 Ƙazantarta tana cikin tufafinta,

Ba ta tuna da ƙarshenta ba,

Domin haka faɗuwarta abar tsoro ce,

Ba ta da mai yi mata ta’aziyya.

“Ya Ubangiji, ka dubi wahalata,

Gama maƙiyi ya ɗaukaka kansa!”

10 Maƙiyi ya miƙa hannunsa

A kan dukan kayanta masu daraja,

Gama ta ga al’ummai sun shiga Haikali,

Su waɗanda ka hana su shiga cikin jama’arka.

11 Dukan jama’arta suna nishi don neman abinci,

Sun ba da kayansu masu daraja saboda abinci

Don su rayu.

“Ya Ubangiji ka duba, ka gani,

Gama an raina ni.”

12 “Dukanku masu wucewa, ba wani abu ba ne a gare ku?

Ku duba, ku gani, ko akwai baƙin ciki irin nawa,

Wanda Ubangiji ya ɗora mini,

A ranar fushinsa mai zafi.

13 “Daga sama ya aukar da wuta a cikin ƙasusuwana.

Ya kuma kafa wa ƙafafuna ashibta,

Ya komar da ni baya,

Ya bar ni a yashe, sumamme dukan yini.

14 “Ubangiji ya tattara laifofina

Ya yi karkiya da su,

Ya ɗaura su a wuyana,

Ya sa ƙarfina ya kāsa.

Ya kuma bashe ni a hannun

Waɗanda ban iya kome da su ba.

15 “Ubangiji ya yi watsi da majiya ƙarfina,

Ya kirawo taron jama’a a kaina

Don su murƙushe samarina.

Ya kuma tattake Urushalima, zaɓaɓɓiyarsa,

Kamar ‘ya’yan inabi a wurin matsewa.

16 “Ina kuka saboda waɗannan abubuwa,

Hawaye suna zuba sharaf-sharaf daga idanuna.

Gama mai ta’azantar da ni,

Wanda zai sa in murmure yana nesa da ni.

‘Ya’yana sun lalace,

Gama maƙiyi ya yi nasara!”

17 Sihiyona tana miƙa hannuwanta,

Amma ba wanda zai ta’azantar da ita.

Gama Ubangiji ya umarci maƙwabtan Yakubu su zama maƙiyansa.

Urushalima kuma ta zama ƙazantacciya a tsakaninsu.

18 “Abin da Ubangiji ya yi daidai ne,

Gama ni na ƙi bin maganarsa,

Ku ji, ya ku jama’a duka,

Ku dubi wahalata,

‘Yan matana da samarina,

An kai su bauta!

19 “Na kira masoyana, amma suka yaudare ni,

Firistocina da dattawana a cikin birni sun hallaka

Saboda neman abincin da za su ci su rayu.

20 “Ka duba, ya Ubangiji, ina shan wahala,

Raina yana cikin damuwa,

Zuciyata tana makyarkyata saboda tayarwata.

A titi takobi yana karkashewa,

A gida kuma ga mutuwa.

21 “Sun ji yadda nake nishi,

Ba mai ta’azantar da ni.

Dukan maƙiyana sun ji labarin wahalar da nake ciki,

Suna kuwa murna da ka yi haka.

Ka kawo ranan nan da ka ambata,

Domin su ma su zama kamar yadda nake.

22 “Ka sa mugayen ayyukansu su bayyana a gabanka,

Sa’an nan ka hukunta su kamar yadda ka hukunta ni saboda dukan laifofina.

Gama nishe-nishena sun yi yawa.

Zuciyata kuma ta karai.”