AMOS 3

Aikin Annabi

1 Jama’ar Isra’ila, ku kasa kunne ga wannan saƙo da Ubangiji ya aiko muku, ya ce, “Na fitar da iyalanku duka daga Masar.

2 Daga cikin dukan al’umman da nake

ƙauna a duniya,

Ku kaɗai ne na sani,

Nake kuma kulawa da ku,

Don haka zan hukunta ku saboda

zunubanku.”

3 Zai yiwu a ce mutum biyu za su yi

tafiya tare,

Amma su rasa shirya magana?

4 Zai yiwu zaki yă yi ruri a jeji

Ba tare da ya kama nama ba?

Zai yiwu sagarin zaki yă yi gurnani a

kogonsa

In bai kama wani abu ba?

5 Zai yiwu tsuntsu ya fāɗi ƙasa

In ba a kafa masa tarko ba?

Zai yiwu tarko ya zargu

In bai kama wani abu ne ba?

6 Zai yiwu mutane su rasa firgita,

Idan aka busa ƙahon yaƙi a

birni?

Zai yiwu wata babbar masifa ta auko

wa birni

Ba da yardar Ubangiji ba?

7 Hakika Ubangiji ba yakan aikata

kome ba,

Sai da sanin bayinsa annabawa.

8 Zaki ya yi ruri!

Wa ba zai ji tsoro ba?

Sa’ad da Ubangiji ya yi magana!

Wa zai ƙi yin shelar maganarsa?

Faɗuwar Samariya

9 Ka yi shela ga mazaunan fādar Ashdod da Masar, ka ce, “Duk ku taru a Samariya ku ga irin babban shashancin da ake yi a can, ku ga irin laifofin da ake aikatawa a birnin.”

10 Ubangiji ya ce, “Waɗannan mutane suka cika gidajensu masu daraja da abubuwan da suka samo ta hanyar zamba, da ta kama-karya. Ta yadda za su yi su yi aminci ma, ba su sani ba.

11 “Saboda haka abokan gaba za su

kewaye ƙasarsu,

Su hallakar da kagaransu,

Su washe gidajen nan nasu masu

daraja.”

12 Ubangiji ya ce,

“Kamar yadda makiyayi yakan ceci

ƙafafu biyu

Ko kunne ɗaya na tunkiya daga

bakin zaki,

Haka nan kuma kima daga cikin

mutanen Samariya

Waɗanda suke zaman jin daɗi za su

tsira.

13 Ku saurara yanzu,

Ku yi wa zuriyar Yakubu kashedi,”

In ji Ubangiji, Maɗaukaki.

14 “Ran da na hukunta mutanen

Isra’ila saboda zunubansu,

Zan hallakar da bagadan Betel.

Za a kakkarya zankayen bagaden,

Su fāɗi ƙasa.

15 Zan murmushe gidajensu na rani da

na damuna.

Zan hallakar da gidajen da aka

ƙawata da hauren giwa,

Kowane babban gida kuwa za a

rushe shi.”