AMOS 5

Kira Zuwa Tuba

1 Ku kasa kunne, ku jama’ar

Isra’ila, ga waƙar makoki da zan yi

a kanku.

2 Isra’ila ta fāɗi,

Ba kuwa za ta ƙara tashi ba.

Tana fa kwance a ƙasa,

Ba wanda zai tashe ta.

3 Ubangiji ya ce,

“Wani birnin Isra’ila ya aika da soja

dubu,

Ɗari ne kaɗai suka komo,

Wani birni kuma ya aika da soja ɗari

ne,

Amma goma kaɗai suka komo.”

4 Ubangiji ya ce wa jama’ar Isra’ila,

“Ku zo gare ni, za ku tsira.

5 Kada ku tafi ku yi sujada a Biyer-

sheba.

Kada ku yi ƙoƙarin nemana a

Betel,

Gama Betel lalacewa za ta yi.

Kada ku tafi Gilgal,

Gama an ƙaddara wa jama’arta su

yi ƙaura.”

6 Ku tafi wurin Ubangiji ku tsira.

Idan kuwa kun ƙi,

Shi zai babbaka jama’ar Yusufu

Kamar yadda a kan babbaka da

wuta.

Wuta za ta ƙone jama’ar Betel,

Ba kuwa mai kashe wutar.

7 Abin tausayi ne ku da kuke ɓata

shari’a,

Kuna hana wa mutane hakkinsu.

8 Ubangiji ne ya yi taurarin

Kaza da ‘ya’yanta

Da mai farauta da kare.

Ya mai da duhu haske,

Rana kuwa dare.

Shi ya kirawo ruwan teku ya

bayyana,

Ya shimfiɗa shi a bisa ƙasa.

Sunansa Ubangiji ne.

9 Ya kawo halaka a kan ƙarfafa,

Da a kan birane masu garu.

10 Kun ƙi wanda ya tsaya a kan

adalci,

Da mai faɗar ainihin gaskiya a gaban

shari’a.

11 Kun matsa wa talakawa lamba,

Kun ƙwace musu abincinsu.

Saboda haka kyawawan gidajen nan

da kun gina da dutse,

Ba za ku zauna a cikinsu ba,

Ba kuwa za ku sha ruwan inabin

nan

Daga kyawawan gonakin inabinku

ba.

12 Na san irin zunuban da kuke yi,

Da mugayen laifofin da kuka aikata.

Kuna wulakanta mutanen kirki,

Kuna cin hanci,

Kuna hana a yi wa talakawa shari’ar

adalci a majalisa.

13 Ashe, ba abin mamaki ba ne,

Da masu hankali suka kame bakinsu

A waɗannan kwanaki na mugunta.

14 Ku yi ƙoƙari, ku yi nagarta, ba

mugunta ba,

Domin ku tsira.

Sa’an nan ne Ubangiji Allah

Maɗaukaki

Zai kasance tare da ku sosai,

Kamar yadda kuka ɗauka!

15 Ku ƙi mugunta, ku ƙaunaci

nagarta,

Ku yi adalci cikin majalisar

alƙalanku!

Watakila Ubangiji Allah Mai

Runduna

Zai yi wa sauran da suka ragu na

wannan al’umma alheri.

16 Haka Ubangiji Allah Mai Runduna

ya ce,

“Za a yi kuka, a yi kururuwa a

titunan birninku saboda azaba.

Daga ƙauyuka za a kirawo

mutane

Su zo su yi makokin.

Waɗanda suka mutu, tare da masu

makoki da aka ijarar da su.

17 Za a yi kuka ko’ina cikin dukan

gonakin inabinku

Gama zan zo in yi muku horo.”

18 Taku ta ƙare, ku da kuke marmarin

zuwan ranan nan ta Ubangiji!

Wane amfani wannan rana za ta yi

muku?

Rana ta baƙin ciki ce,

Ba ta murna ba.

19 Zai zama kamar wanda ya tsere wa

zaki

Ya fāɗa a bakin beyar!

Ko kuwa kamar wanda ya komo

gida,

Ya dāfa bango, maciji ya sare shi.

20 Ranar Ubangiji za ta kawo baƙin

ciki,

Ba murna ba.

Rana ce ta damuwa ba ta fara’a ba.

21 Ubangiji ya ce,

“Na ƙi bukukuwanku na addini.

Ina ƙyamarsu!

22 Sa’ad da kuka kawo mini hadayun

ƙonawa

Da hadayunku na tsaba, ba zan

karɓa ba.

Ba kuma zan karɓi turkakkun

dabbobinku

Waɗanda kuka miƙa mini hadayun

godiya ba.

23 Ku yi shiru da yawan hargowar

waƙoƙinku.

Ba na so in saurari kaɗe-kaɗenku da

bushe-bushenku.

24 Sai ku sa adalci da nagarta su gudano

a yalwace

Kamar kogin da ba ya ƙafewa.

25 “Ya ku, jama’ar Isra’ila, ai, a waɗannan shekaru arba’in da kuka yi cikin jeji kuka kawo mini sadaka da hadayu,

26 duk da haka, kuka ɗauki siffofin gumakanku na taurari, wato Sakkut da Kaiwan, waɗanda kuka yi wa kanku.

27 Ni kuwa zan sa ku yi ƙaura zuwa wata ƙasa gaba da Dimashƙu.” Ubangiji, Allah Mai Runduna, shi ne ya faɗa.