MIKA 3

An Yi wa Shugabannin Isra’ila Faɗa

1 Ni kuwa na ce, “Ku ji, ya ku

shugabannin mutanen Yakubu,

Da ku sarakunan Isra’ila.

Ya kamata ku san shari’a.

2 Amma kuna ƙin nagarta, kuna

ƙaunar mugunta,

Kuna feɗe mutanena,

Kuna kuma fizge naman jikinsu daga

ƙasusuwansu.

3 Kuna cin naman mutanena, kuna

feɗe fatar jikinsu,

Kuna kakkarya ƙasusuwansu,

Kuna yanyanka su gunduwa

gunduwa kamar naman da za a sa

a tukunya.”

4 Sa’an nan za su yi kuka ga Ubangiji,

Amma Ubangiji ba zai amsa musu

ba.

Zai ɓoye musu fuskarsa a wannan

lokaci,

Saboda mugayen ayyukansu.

5 Ga abin da Ubangiji ya ce a kan

annabawan da suka bi da

mutanensa a karkace,

Waɗanda suke cewa, “Salama,”

sa’ad da suke da abinci,

Amma sukan kai yaƙin shahada

Ga wanda bai ba su abin sawa a baka

ba.

6 Saboda haka kome zai zama dare

da duhu, ba wahayi ko duba.

Rana za ta fāɗi a kan annabawa,

Yini zai zama musu duhu baƙi

ƙirin.

7 Masu gani za su sha kunya,

Masu duba kuwa za su ruɗe,

Dukansu za su rufe bakinsu,

Gama ba amsa daga wurin Allah.

8 Amma ni ina cike da iko,

Da Ruhun Ubangiji,

Da shari’a da ƙarfin hali,

Don in sanar wa Yakubu da laifinsa,

Isra’ila kuma da zunubinsa.

9 Ku ji wannan, ya ku shugabannin

jama’ar Yakubu,

Da ku sarakunan mutanen Isra’ila,

Ku da kuke ƙyamar shari’ar gaskiya,

Kuna karkatar da dukan gaskiya.

10 Kuna gina Sihiyona da jini,

Kuna kuwa gina Urushalima da

zalunci.

11 Shari’ar shugabannin ƙasar ta cin

hanci ce.

Firistocinta suna koyarwa don

neman riba,

Haka kuma annabawa suna annabci

don neman kuɗi.

Duk da haka suna dogara ga

Ubangiji, suna cewa,

“Ai, Ubangiji yana tsakiyarmu,

Ba masifar da za ta same mu.”

12 Saboda ku kuwa za a nome Sihiyona

kamar gona,

Urushalima kuwa za ta zama tsibin

kufai,

Dutse inda Haikali yake zai zama

kurmi.