ZAB 124

Allah Ne Mai Ceton Jama’arsa

1 Da a ce Ubangiji ba ya tare da mu,

Da me zai faru?

Ba da amsa, ya Isra’ila!

2 “Da a ce Ubangiji ba ya tare da mu,

A lokacin da abokan gābanmu suka auka mana,

3 Da sun haɗiye mu da rai a lokacin nan,

Saboda zafin fushi da suke yi da mu,

4 Da rigyawa ta kwashe mu,

Da ruwa yi ci mu,

5 Kwararowar ruwa ya nutsar da mu.”

6 Sai mu gode wa Ubangiji,

Da bai bar abokan gābanmu su hallaka mu ba.

7 Mun kuɓuta kamar tsuntsu daga tarkon mai farauta,

Tarkon ya tsinke, mun ‘yantu!

8 Taimakonmu daga wurin Ubangiji yake zuwa,

Shi wanda ya yi sama da duniya.