ZAB 125

Zaman Lafiyar Jama’ar Allah

1 Waɗanda suke dogara ga Ubangiji,

Suna kama da Dutsen Sihiyona,

Wanda ba zai jijjigu ba, faufau.

Faufau kuma ba za a kawar da shi ba.

2 Kamar yadda duwatsu suka kewaye Urushalima,

Haka nan Ubangiji zai kewaye jama’arsa,

Daga yanzu har abada.

3 Ba a koyaushe mugaye za su yi mulki a ƙasar jama’ar Allah ba,

Idan kuwa suka yi, to, ya yiwu jama’ar Allah su yi laifi.

4 Ya Ubangiji, ka yi wa mutanen kirki alheri,

Su waɗanda suke biyayya da umarnanka!

5 Amma ka hukunta waɗanda suke bin mugayen al’amuransu,

Sa’ad da kake hukunta wa masu aikata mugunta!

Salama ta kasance tare da Isra’ila!