ZAB 126

Godiyar Samun Ceto

1 Sa’ad da Ubangiji ya komar da mu cikin Sihiyona,

Sai abin ya zama kamar mafarki!

2 Muka kece da dariya, muka raira waƙa don farin ciki,

Sa’an nan sai sauran al’umma suka ambace mu, suka ce,

“Ubangiji ya yi manyan al’amura masu girma, sabili da su!”

3 Hakika ya aikata manyan al’amura sabili da mu,

Mun kuwa yi farin ciki ƙwarai!

4 Ya Ubangiji, ka komar da mu ƙasarmu

Kamar yadda ruwan da kake yi yakan koma cikin busassun koguna,

5 Ka sa waɗanda suke kuka a lokacin da suke dashe,

Su tattara albarkar kaka da farin ciki!

6 Su waɗanda suka yi kuka a sa’ad da suka fita suna ɗauke da iri,

Za su komo ɗauke da albarkar kaka,

Suna raira waƙa don farin ciki!