ZAB 127

Yabon Alherin Ubangiji

1 Idan ba Ubangiji ne ya gina gidan ba,

Aikin magina banza ne.

Idan ba Ubangiji ne ya tsare birnin ba,

Ba wani amfani a sa matsara su yi tsaro.

2 Ba wani amfani a sha wahalar aiki saboda abinci,

A yi asubancin tashi, a yi makarar kwanciya,

Gama Ubangiji yakan hutar da waɗanda yake ƙauna.

3 ‘Ya’ya kyauta ne daga wurin Ubangiji,

Albarka ce ta musamman.

4 ‘Ya’ya maza da mutum ya haifa a lokacin ƙuruciyarsa

Kamar kibau suke a hannun mayaƙi.

5 Mai farin ciki ne mutumin da yake da irin waɗannan kibau da yawa!

Faufau ba za a ci nasara a kansa ba,

Sa’ad da ya kara da maƙiyansa a wurin shari’a.