ZAB 128

Albarkar Mai Tsoron Ubangiji

1 Mai farin ciki ne wanda yake tsoron Ubangiji,

Wanda yake zamansa bisa ga umarnansa!

2 Za ka sami isasshen abin biyan bukatarka,

Za ka yi farin ciki ka arzuta.

3 Matarka za ta zama kamar kurangar inabi

Mai ‘ya’ya a gidanka,

‘Ya’yanka maza kuma kamar dashen zaitun

Suna kewaye da teburinka.

4 Mutumin da yake yi wa Ubangiji biyayya,

Hakika za a sa masa albarka kamar haka.

5 Ubangiji ya sa maka albarka daga Sihiyona!

Ya sa ka ga Urushalima ta arzuta

Dukan kwanakinka!

6 Ya kuma sa ka ka ga jikokinka!

Salama ta kasance ga Isra’ila!